Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul Baiti (AS) – ABNA: Bukatu da Sha’awa da dandanon daidaikun mutane a kowane lamari sun sha bamban, don haka dogaro da sha’awar daidaikun mutane a kowane hali, ciki har da aure, yana kawo wahala. Domin magance matsalar zabar aure yana da kyau mutum ya yi dubi ga shiriyar ma'asumai.
A nan za mu ambaci wasu daga cikin sifofin miji na qwarai ta fuskar yadda ma’asumai As suke ganin yafi dacewa:
1. Ya Kasance Mai Tarbiyya Da Kyawawan Halaye.
Hussain Bashar yana cewa: Na rubuta wa Imami na Bakwai cewa wani daga cikin dangina ya nemi 'yata, amma halinsa ba shi da kyau. Sai imam ya ce: Idan ya kasance mai mugun hali kada ka ka hada auratayya da shi. (1)
2. Ya Kasance Mai Takawa Da Tsoron Allah Ne.
Wani mutum ya zo wajen Imam Hasan Mujtaba (a.s.) domin ya shawarce shi game da auren 'yarsa. Sai imam ya ce masa: “Ka aurar da ita ga mai tsoron Allah, domin idan yana sonta sai ya girmama ta, idan kuma ya qi ta to ba zai zalunce ta ba (2).
«زَوِّجْها مِنْ رَجُلٍ تَقیّ فَاِنَّهُ اِنْ اَحَبَّها اَکْرَمَها واِنْ اَبْغَضَها لَمْ یَظْلِمْها؛
3. Kada Ya Kasance Mai Shan Giya.
Imami na takwas (a.s) ya ce: “Ya wajaba a gare ku da ku guji aurar da [’yarku] ga mai shan giya, domin idan kuka aurar da ita ga mai shan giya, kamar kun kai ta ne zuwa ga haram.” (3).
4. Kada Ya Zama Mai Aikata Zunubi.
Manzon Allah (s.a.w) ya ce: “Duk wanda ya aurar da ‘yarsa ga wani fasiki, la’ana dubu za ta sauka a kansa kowace rana.” (5).
Madogara:
1. Biharul-Anwar, juzu'i. 103, ku. 235.
2. Makarimul-Akhlaq, shafi. 204.
3. Biharul-Anwar, juzu'i. 79, ku. 142.
4. Dr. Ghiyathud-Din Jazayeri, I’ijazul-Khurakiha, shafi. 214.
5. Mustadrakul-Wasayl, juzu'i. 14, ku. 192.
Your Comment